IQNA

22:56 - November 16, 2016
Lambar Labari: 3480946
Bangaren kasa da kasa, Al'ummar yankin Lisasafah da ke cikin gundumar kazablanka a kasar Morocco sun gudanar da wani gangami a yau domin nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a yankin.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na Nur Press ya habarta cewa, an samu wasu kwafi-kwafin alkur'ani mai tsarki a yagea cikin masallaci Alkhuzami da ke yankin Lisasafah a cikin gundumar Kazablanka a kasar Morocco, lamarin da ya harzuka al'ummar yankin baki daya.

Rahoton ya ce jama'a sun taru suna yin kira ga hukumomin kasar ta Morocco da su dauki matakan gagagwa wajen gano tare da hukunta duk wanda aka samu da laifin keta alfarmar kur'ani mai tsarki a wanann masallaci, wanda shi ne karo na biyar da hakan ta faru a cikin wannan wata a cikin yankin.

Limamin masallacin Alkhuzami ya ce bayan kammala sallar Isha'in jiya, wata mata ta zo ta tambaye bangaren da mata ke salla cikin masallacin, kuma bayan ta fita ne aka samu kur'anai da dama an keta su a cikin masallacin a bangaren mata.

3546416


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، Morocco ، kazablanka ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: