IQNA

21:46 - November 24, 2016
Lambar Labari: 3480968
Bangaren ksa da kasa, cibiyar yada al'adun muslunci ta isar da sakon ta'aziyyar rasuwar Ayatollah Musawi Ardabili.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar yada al'adun muslunci cewa, cibiyar ta fitar da bayani kamar haka:

Da Sunan Allah Madaukaki

Idan malami ya rasu an yi rashia cikin muslunci da babu abin da zai maye gurbinsa.

Hakika labarin rasuwar babban malamin addinin muslunci kamar Ayatollah Ozma Musawi Ardabili, babban rashi ne mai daga hankali matuka ga dukkanin masu son juyin islama.

Shi mutum ne da ya kasance mai sadaukantarwa domin addininsa da al'ummarsa, ya yi gwagwarmaya tare da mara baya ga jagoran juyin Islam marigayi Imam Khmenei (RA) kamar yadda kuma ya kasance abin buga misali ta fuskar adalci a lokacin da ya rike mukamin alkalin alkalai na kasa baki daya bayan juyin muslunci.

Cibiyar yada al'adun muslunci tana isar da sakon ta'aziyya ga iyalan wannan bban malami bisa wannan rashi da al'ummar musulmi ta yi baki daya, kamar yadda kuma cibiyar take mika sako ga cibiyar ilimi ta birnin Qom a jamhuriyar muslunci.

3548443


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: