IQNA

20:55 - November 25, 2016
Lambar Labari: 3480971
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da mayar da martani dangane da hare-haren ta’addanci da aka kai a Iraki daga ciki kuwa har da martanin kungiyar Hizbullah.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alalam cewa, jamhuriyar musulinci da Kungiyar Hizbullah ta kasar Labnon, Kasashen Masar, Burtaniya da Amurka sun yi alawadai kan harin ta'addancin da aka kai Iraki tare kuma da tabbatar da yakar kungiyar IS.

A jiya Alkhamis ne, wata mota shake da bama-bamai ta tarwatse a wurin shan Mai na anguwar Alshumaly na garin Halah babban birnin Jihar babul dake kudancin Bagdaza, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar mutane 80 da kuma jikkatar wasu sama da 20 na daban daga cikin wadanda suka ziyarci Imam Husain (a.s).

A cikin wani jawabi da ya gabatar a daren jiya Alkhamis, Fu'ad Ma'asum Shugaban kasar Iraki ya yi alawadai da wannan mumunan harin ta'addanci tare da bayyana shirin jami'an tsaro da Al'ummar kasar wajen karya lagon 'yan ta'addar a kasar.

Bahram Kasimi kakakin Ma'aikatar harakokin wajen Iran ya yi alawadai da wannan ta'addanci tare da meka ta'aziyarsa ga iyalan wadanda harin ya ritsa da su, sannan ya ce hari ya biyo bayan kashin da 'yan ta'adda ke sha a hanun Dakarun tsaron kasar, kuma Jumhoriyar musulinci ta Iran za ta tsaya tsayin daka a bayan Gwamnati da kuma Al'ummar Iraki wajen yaki da ta'addanci.

A bangare guda Gwamnatin kasar Masar da kuma Kungiyar Hizbul... ta kasar Labnon sun fitar da sanarwa inda suka yi alawadai da wannan hari na ta'addanci tare da meka ta'aziyar su ga iyalan wadanda harin ya ritsa da su.

A nasa bangare, Mataimakin Ministan harakokin wajen Burtaniya Tobias L. Wood cikin wata sanarwa da ya yi a daren jiya Alkahmis ya yi alawadai da wannan ta'addanci sannan ya bayyana shi a matsayin dabbanci.

Wakilin Shugaban Amurka na musaman a kawancen yaki da kungiyar IS ya rubuta a shafin sadarwa sa na Twiter cewa Watsinton ta yi alawadai da kisan fararen hula wadanda ba su ji ba su gani ba, domin tabbatar da adalci wajen yakar IS, Amurka za ta kasance a bangaren Gwamnatin kasar Iraki.

3548662


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: