IQNA

Masu Hidima A Hubbaren Hussaini Sun Yi Bakwana

20:24 - December 01, 2016
Lambar Labari: 3480991
Bangaren kasa d akasa, masu hidima a hubbaren Imam Hussain (AS) a Karbala lokacin tarukan muharram da safar da suka hada da masu wakokin yabo da bakin ciki sun yi bankwana.

Kmafanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin Alfurat News cewa, gungun mawaka da masu hidima a hubbaren Karbala sun yi bankawana a lokacin da watannin bakin ciki suka kawo karshe.

Bisa ga wannan rahoto, masu hidimar bayan kammala sallolin magariba da isha’i sun nufi babul kibla da ke cikin hubbaren mai tsarki, inda daga nan suka fara zuwa kuma aka kammala a hubbaren Abbas (AS).

Masu hidimar sun kammala taron nasu na bankwana ne da makoki ga bayan karewar watannin muharram da safar, inda aka tattara dukkanin abubuwan da aka saka na juyayin shahadar iyaklan gidan manzo da kuma wafatin manzon tsira.

An janye bakaken tutocin da aka kafa tun farkon watan muharram, inda aka saka tutoci na murnar haihuwar manzon Allah, a farkon wanna wata na rabiul awwal, kuma za a ci gaba da tarukan murnar haihuwar mafificin hallitun ubangiji a cikin wannan wata mai alfarma.

3550165

Masu Hidima A Hubbaren Hussaini Sun Yi Bakwana

Masu Hidima A Hubbaren Hussaini Sun Yi Bakwana

Masu Hidima A Hubbaren Hussaini Sun Yi Bakwana

Masu Hidima A Hubbaren Hussaini Sun Yi Bakwana

captcha