Bangaren kasa da kasa, Wani hamshakin mai kudi a kasar Amurka kuma daya daga cikin yahudawa masu kare manufofin Isra'ila a Amurka, ya tsaya kai da fata domin ganin an hana wani dan majalisar dattijan kasar musulmi rike shugabancin kwamitin zartarwa na jam'iyyar Democrat.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya
habarta cewa, ya nakalto daga Tashar talabijin ta PressTV ta bayar da rahoton
cewa, hamshakin mai kudi a kasar Amurka kuma bayahuden Isra'ila Haim Saban,
wanda ya kashe daruruwan miliyoyin daloli wajen yakin neman zaben 'yar takarar
shugabancin Amurka ta jam'iyyar Democrat Hillary Clinton, ya bayyana rashin
amincewarsa da duk wani yunkuri na nada Kitt Alison wani musulmi dan majalisar
dattijai daga jahar Minnesota a matsayin shugaban kwamitin zartarawa na
jam'iyyar Democrat.
A nata bangaren tashar CNN ta bayar da rahoton
cewa, Kitt Alison ya gabatar da wani jawabi a birnin Washington, wanda kuma
jawabin nasa na kunshe da sukar salon siyasar Isra'ila, tare da nuna kin jinin
yahudawan Isra'ila.
Wata kungiyar yahudawan Amurka masu goyon bayan
Isra'ila ADL ta dauko wani bayanin da Alison ya yi a cikin sheakara ta 2010,
inda ta ce yana sukar Isra'ila kai tsaye, wanda hakan ya yi hannun riga da
salon siyasar jam'iyyar Democrat, wadda ta ginu a kan kare dukkanin manufofin
Isra'ila, a kan haka su ma suna kira da kada abari ya karbi kwamitin zartarwa
na jam'iyyar.
3550723