A ranar 16 ga watan Oktoban da ya gabata ne wata babbar kotu a kasar Bahrain din ta yi watsi da hukuncin farko na daurin shekaru 9 da wata kotu ta yanke Sheik Ali Salman din da kuma bukatar a sake shari'ar da aka yi masan, inda kotun daukaka karar a yau ta tabbatar da hukuncin da kotun farko din ta yanke.
Tun a jiya dai al'ummomin kasar Bahrain din suke gudanar da zanga-zanga da gangami don nuna rashin amincewarsu da hukunci da kotun daukaka karar take shirin yankewa a yau.
A watan Disamban 2014 ne dai mahukuntan kasar Bahrain din suka kama Shiek Ali Salman bisa zargin hada baki da 'yan kasashen waje wajen kifar da gwamnatin Bahrain din, lamarin da Shehin malamin ya musanta. Kungiyoyin kare hakkokin bil'ama na kasa da kasa suna ci gaba da Allah wadai da ci gaba da tsare Sheik Salman da sauran 'yan Shi'a na kasar da gwamnatin take musguna musu.