Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga bangaren sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, a jiya an bude baje kolin kur’ani mai tsarki wanda karamin ofishin jakadancin Iran ya shirya a birnin Pretoria na kasar Afirka ta kudu.
An gudanar da wannan baje koli ne a masallacin Centre Pretoria, daya daga cikin manyan masallatai da ke birni, an kuma nuna nauoin kwafin kur’ani a wurin, da suka hada har da wani kwafin kur’ani mai rubutu da lanu 9, da kuma wadanda aka tarjamaa cikin harsuna 10 rayyau na duniya.
A lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban daruruwan mutanen da suka tarua wurin, jakadan kasar Iran Sharuz Falahat Pishe ya bayyana cewa, wannan baje koli shi ne irinsa na farko, kuma ya kara fito da abubuwa masu matular muhimamnci da musulmi suke da si da suka danganci kur’ani, domin baya ga kwafin kur’ani, an nuna wasu alluna da aka kayata da rubtu mai kyau na ayoyin kur’ani da ke daukar hankali.
Ya ce ko shakka babu bayan samun narar juyin juya halin musluncia Iran, an mayar da hankali matuka kana bin da ya shafi kur’ani mai tsarki da kuma koyarwarsa, wanda hakan ne ya sanya ahlin yanzu Iran take gudanar da irin wannan baje a koli na kur’ani a kasashen duniya daban-daban, domin yada ilimin kur’ani da sakonsa zuwa kowace kusurwa ta duniya.
Sharuz Falah Pishe daga karshe ya yabawa dukaknin wadanda suka taiomaka wajen ganin wanann shiri na baje koli ya gudana a cikin nasara, tare da kuma taya al’ummar musulmi muranar maulidin manzon Allah (SAW) da ake gudanarwa a cikin wadannan kwanaki masu albarka.