IQNA

Daurin Shekaru 4 A Gidan Kaso Kan Mai Wulakanta Kur'ani

23:52 - December 25, 2016
Lambar Labari: 3481068
Bangaren kasa da kasa, wata kotu a birnin kazablanka na kasar Morocco ta daure wata mata mai wulakanta kur'ani shekaru 4 a gidan kaso.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hespress.com cewa, kotun ta Kazablanka ta yanke hukuncin ne a kan wannan mata bayan da ta wulakanta kur'ania acikin wasu masallatai a yankin Lisasafaha tare da tara da dirhami 500.

Wannan mata dai wadda ta kai kimanin shekaru 40 da haihuwa, tana shiga cikin masallatai ne a lokacin da ta lura da cewa ba a ganinta, sai ta keta kwafin kur’anai da ke cikin masallatan.

Ta yi hakana wasu masallati amma ba a iya gano ta ba, sai a lokacin da ta yi hakan a masallacin Lisasafa, inda limamnin masalacin da kansa ne ya lura da cewa ta shiga bangaren mata bayan kammala sallar isha’I, kuma alokacin babu kowa a ciki, bayan ta fita sai aka ga an yaga kur’anai a da ke wurin.

Yanzu haka dai an kame ta kuma an gurfanar da ita agaban kuliya, inda kotu ta yanke mata hukuncin daurin shekaru hudu a jerea gidan kaso, tare da biyan tara, an yi hakan ne domin ya zama darasi gad k wani mai tunanin yin irin aikin da ta yi na keta alfarmar kur’ani mai tsarki.

3556548/4



captcha