IQNA

23:18 - January 18, 2017
Lambar Labari: 3481146
Bangaren kasa da kasa, Antonio Guterres a cikin wani jawabinsa ya yi ishara da aya ta 13 a cikin surat Hujrat da ke tabbatar da cewa kur’ani yana yin kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna atsakanin ‘yan mutane.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, sabon babban sakataren majalisar dinkin duniya tsohon jami’in diflomasiyyar kasar Portugal, ya bayyana shekara ta 2017 a matsayin shekara ta zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummomin duniya.

Antonio Guterres ya bayyana hakan ne a wani taro da aka shirya a birnin New York na kasar Amurka domin nuna adawa da kyamar da ake nuna wa musulmi a Amurka da ma wasu kasashen duniya.

Ya ce ko shakka babu akwai abubuwa da suke faruwa da ba su da dadin ji, na kyma da ake nuna wa wasu a duniya, ko dai saboda addininsu ko launin fatarsu ko abin da ya yi kama haka, har ma da cin zarafinsu, kuma akwai irin wadannan abubuwa da suka faru a wasu wuraren wadanda ba ji labari ba.

Sabon babban sakataren majalisar dinkin duniya ya ce zai iyakacin kokarinsa domin ganin an takawa cin zarafin dan adam birki a duniya, tare da kare hakkokinsa da akidarsa da mutuncinsa, da rayuwarsa da karamarsa.

Haka nan kuma ya yi ishara da fadar kur’ani a cikin aya ta 13 surat Hujrat, da ke bayyana cewa Allah ya halicci mutane maza da mata ya sanya su al’ummomi da kabilu domin su fahimci junansu.

Daga karshe ya ce aikin dawo da zaman lafiya da sulhu a tsakanin al’ummomin duniya aiki ne da ya rattaya a kan kowa, saboda zai yi aiki ne tare da al’ummomi ba tare da mayar da wani saniyar ware ba, domin a samu zaman lafiya da sulhu a duniya.

3564015


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: