IQNA

Malamin Azhar Ya Maida Martani kan Katse Karatun Kur’ani A Tashar Talabijin

22:49 - January 20, 2017
Lambar Labari: 3481154
Bangaren kasa da kasa, mai gabatar da wani shirin a tashar DW ya jawo fushin Sheikh Ahmad karima daya daga cikin fitattun malaman cibiyar Azhar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Almisriyun cewa, an shirya wani shiri ne a tashar talabijin ta kasar Jamus Deutsche Welle, inda Sheikh Ahmad Karima zai gabatar da bayani a kan aure.

A lokacin da yake fara bayaninsa ya fara da karatun wata ayar kur’ani mai tsarki, a nan take sai mai gabatar da shirin ya katse shi, lamarin da ya jawo fushin shehin malamin, inda ya tambaye shi cewa ko shi ba musulmi ba ne, domin karatun ayar kur’ani mai tsarki da take da laka da abin da za a yi Magana babu wata matsala a cikinsa.

Wannan ya sanya shi ma mai gabatar da shirin ya fusata, inda ya ce da Sheikh Ahmad Karimah kai baka da ikon ka gaya mani addinin muslunci, ina gudanar da aikina ne kawai, daga lokacin da na shigo nan babu batun addini ko akida, du kina ajiye su gefe guda ne.

Sakamakon wannan cacar baki, Sheikh Ahmad Karima ya fice daga dakin watsa shirye-shiryen, ya kuma ce da mai gabatar da shirin kada ya kara tuntubarsa daga rana irin ta yau, domin kuwa shi addininsa shi ne gaba da komai, duk abin da babu addini a cikinsa ba shi a ciki.

An shirya cewa wannan babban malamin shari’a na cibiyar Azhar zai yi Magana ne kan wasu batutuwa da suke da alaka da aure a mahangar shari’ar muslunci.

3564568


captcha