IQNA

23:00 - January 22, 2017
Lambar Labari: 3481160
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Masar ta jibge daruruwan jami’an tsaro domin hana gudanar da tarukan mabiya mazhabar shi’a na kasar ke gudanarwa a masalalcin Imam Hussain (AS) a birnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na «bwabtk.com» cewa, gwamnatin kasar Masar tare da hadin baki da ‘yan salafiyyah na kasar masu tsananin kiyayya da mazhabar iyalan gidan manzo, sun dauki matakan hana mabiya mazhabar shi’ar ahlul bait gudanar da tarukan da suka saba gudanarwa a wannan lokaci.

Bisa ga al’ada dai mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a Masar suna gudanar da taruka a wannan lokaci da suke cewa a wannan lokaci ne aka kawo kan Imam Hussain (AS) aka bizne shi Masar, inda kuma nan ne ya koma masallacin kan Hussain (AS) daya daga cikin masallatai masu tsohon tarihi da ke birnin Alkahira.

Jami’an tsaro tare da ma’akatar kula da harkokin addini ta kasar wadda ke aiki tare da masu dauke da akidar kafirta musulmi wato takfiriyyun, sun fake da cewa a wannan lokacin ne ake sa ran wasu za su gudanar da taruka tunawa da jiyin juya halin kasar na 25 ga watan Janairun 2011, wanda ya kawo karshen mulkin Husni Mubarak.

A kan mahukuntan an Masar bisa fakewa da wannan hujja suka zuba daruruwan ‘yan sanda a cikin kayan sarki domin hana gudanar da tarukan da ake yi daruruwan shekaru.

Sibt Ibn Jazi daya daga cikin manyan malaman sunnah Imam Hussain  ya rubuta cewa, khalifofin Fatimiyyah da suka mlki Masar, sun dauko kan Imam Hussain (AS) daga Faradis da ke Damascus zuwa Askalan da ke masar, daga bisani aka iso da kan nasa zuwa birnin Alkahira aka a bizne shi.

3565371


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: