IQNA

22:30 - February 12, 2017
Lambar Labari: 3481225
Bangaren kasa da kasa, sakamakon wata gobara da ta tashia cikin masallacin Abdulrahman a yankin Almuddah da ke cikin gundumar Benzurt kur'anai 111 suka kone.

BKamfanin dilalncin labaran IQNA ya habarta cewa ya nakalto daga shafin Anba Tunis cewa, a jiya gobara ta tashia cikin masallacin Abdulrahman Benzurt inda kwafin kur'ani mai tsarki guda 111 suka kone kurmus

Khamis bin Ali shi ne shugaban hukumar kula da ayyukan agajin gaggwa na yankin ya bayyana cewa, gobarar ta shammaci mutane, saboda haka kafin a Ankara ta yi mummunar barna, inda kwafin kur'ani 111 suka kone.

Ya ce mutane sun bayar da gunmawa wajen ganin an kasha gobarar, duk kuwa da cewa ta riga ta kone litatfai da suka hada da kur'anai da kuma dardumu da ke cikin wanann masallaci.

Haka nan kuma ya bayyana cewa har yanzu ba asan takamaimai dalilin faruwan wannan gobara ba, amma dai ana gudanar da bincike domin gano musabbabin haka domin a kiyaye a nan gaba.

Wannan masallaci dai yan adaga cikin dadaddun masallatai na yankin, wanda aka gina daruruwan shekaru da suka gabata, a kan haka ake lissafa a shia cikin masallatai na tarihi a yankin.

3573450


Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Tunisia ، Benzurt ، Amuddah ، gobara ، masallaci
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: