IQNA

16:47 - February 26, 2017
Lambar Labari: 3481264
Bangaren kasa da kasa, magajin garin birnin Boston na kasar Amurka ya nuna rashin amincewarsa da duk wani mataki na takura ma musulmi, tare da shan alwashin taimaka ma musulmi 'yan gudun hijira da suke zaune a birnin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, Shafin yada labarai na bostonglobe ya bayar da rahoton cewa, magajin garin birnin Boston Marty Walsh ya halarci taron da musulmi suka gudanar a babbar cibiyarsu da ke birnin, inda ya tabbatar ba zai taba bari a ci mutunci musulmi a birinin ba.

Yayin da yake mayar da martani a fakaice ga shugaban kasar ta Amurka Donald Trump, magajin garin birnin an Boston ya ce; wasu na cewa idan aka bar musulmi suna da baki 'yan gudun hijira suna shigowa Amurka za su karya tattalin arzikin kasar, kuma suna barazana ga tsaro, Marty Walsh ya ce musulmi ba su barazana ga kowa.

Ya kara da cewa ya san wasu za su soke kan wannan matakin nasa, to amma zabe yana zuwa, a nan kowa zai bayyana matsayinsa akwatin zabe.

3577813


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: