IQNA

23:49 - March 28, 2017
Lambar Labari: 3481354
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila sun kame mutane 11 daga cikin masu gadin masallacin quds mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Palastine cewa, da jijjifin safiyar yau jami’an tsaron yahudawan Isra’ila sun kame masu gadin masallacin su 11, bayan da suka bi su har gidajensu daya bayan daya.

Jami’an tsaron na yahudawan Isra’ila sun ce wadannan mutane ba su kiyaye ka’idojin aikinsu, bisa hujjar cewa sun hana wani babban masani bayahude mai gudanar da bincike a wuraren tarihi gudanar da aikinsa a cikin masallacin quds.

Baya ga hakan sun rusa gidan daya daga cikin masu gadin masallacin mai alfarma da ke yankin Isawiyya a gabashin birnin, bisa hujjar cewa an gina gidan ne ba bisa ka’ida ba.

A kowace shekara a lokacin da idin yahudawa ke karatowa, jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila na daukar matakan takura ma Palastinawa mazauna birnin Quds, sakamakon turjiyar da suke nuna wa a lokacin da yahudawa ke shiga cikin harabar masallacin mai alfarma domin gudanar da bukukuwansu.

3585964

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: