IQNA

Cibiyar Fatawa Ta Masar Ta Yi Allawai Da Keta Alkur'ani A Canada

19:29 - April 04, 2017
1
Lambar Labari: 3481376
Bangaren kasa da kasa, cibiyar bayar da fatawar musulunci a kasar Masar ta yi kakkausar suka da yin Allawadai kan keta alfarmar kur'ani mai tsarki a jami'ar Ontarioa ta kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin bawabatul fajr cewa, cibiyar yaki da kyamar muslunci da ke karkashin cibiyar bayar da fatawa a msar, ta fitar da sanarwa dangane da keta alfarmar kur'ani da wasu daliban jami'ar Ontario ta kasar Canada suka yi.

A cikin bayanin nata, cibiyar ta bayyana cewa, ko shakka babu abin da ya faru yana da alaka ne da nuna kiyayya ga musulmi a kasar ta Canada, wanda kuma hakan abin yin Allawadai ne.

Cibiyar ta ce cin zarafin musulmi ko kuma keta alfarmar kur'ani ba shi ne hanya ta hankali ba wajen nuna rashin rashin amincewa ko korafi a kan wani abu, akwai hanyoyi da dama da za a yi yin hakan ba tare da cin zarafi ko keta alfarmar wani addini ba.

Kamar yadda bayanin ya bayyana cewa, musulmin kasar Canada sun jima suna fuskantar matsaloli na cin fuska, amma hakan ya karu ne a cikin lokutan baya-bayan nan, wanda ya kamata mahukuntan kasar su kara azama wajen bayar da kariya ga musulmi, domin kuwa su ba su tsokani kowa ba, a kan haka babu dalilin da zai sanya su zama ragunan layya.

Wannan lamari dai ya faru ne sakamakon bayar da izini ga daliban makaranta musulmi da su gudanar da sallar Juma'a a cikin makarantu matukar dai suna bukatar hakan a wani yanki na musamman.

A nasa bangaren firayi ministan kasar ta Canada ya bayyana takaicinsa matuka dangane da abin da ya faru, inda y ace gwamnatinsa ba ta taba lamuntar faruwar irin wannan aiki na dabbanci ba.

3586327
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Allah yatai maki musulunci da musulmai
captcha