IQNA

An Girmama Mata Mahardata Kur’ani A Kasar Morocco

23:00 - April 05, 2017
Lambar Labari: 3481377
Bangaren kasa da kasa, an girmama mata mahardata kur’ani mai tsarki da hadisin manzo a garin Burkan na kasar Morocco.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na oujdacity cewa, cibiyar kula da harkokin ilimi ta birnin Burkan ce ta dauki nauyin shirya gasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da wannan taro ne tare da halartar wasu daga cikin jami’an gwamnati da kuma malamai, inda aka mika kyautuka na musamman ga dalibai mata 44 mahardata kur’ani mai tsarki da hadisi.

Garin Burkan na daga cikin biranan kasar Morocco da suke mayar da hankali kan batun kur’ani musaman ma ga mata wadanda suke son karatu da hardar kur’ani a birnin, inda yanzu haka akwai cibiyoyi 79 da suke koyar da karatu da hardar kur’ani a birnin.

Babbar manufar gudanar da wannan taro na bayar da kyauta ta usamman domin girmama dalibai makaranta kuma mahardata kur’ani ita ce ci gaba da kara karfafa gwiwar sauran mata da matasa a kan lamarin kur’ani mai tsarki.

3586994


captcha