Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, jaridar Riyadh ta kasar saudiyya ta bayar da rahoton cewa, an yi tarjamar ne a cikin harsunan Pashtu, Fulatanci, Dari, Tajiki, Dagbani, da kuma Nipali.
Wannan tarjama na daga cikin ayyukan da cibiyar da ke kula da masallacin ma’aiki (SAW) take gudanarwa, kuma ana saka sua cikin kantoci domin jama’a masu magana da wadannan harsuna su amfana da su, yanzu haka dai akwai tarjamar kur’ani a cikin harsuna 55 a cikin wannan masallaci mai albarka.
Abdullah Bin salim Al-aufi shi ne shugaban kwamitin kula da ayyukan tarjama a wannan masallaci mai albarka, ya bayyana cewa za su ci gaba da kara fadada aikin tarjama domin amfanin musulmi da suke magana da harsuna daban-daban, da kuma wadanda suke son sanin abin da kur’ani mai tsarki ya kunsa a cikin harsunansu.