IQNA

Rudunar Sojin Syria: Amurka Da ISIS Da Nusra Front Duk Abu Daya Ne

23:44 - April 07, 2017
Lambar Labari: 3481385
Bangaren kasa da kasa, rundunar sojin Syria ta sanar da cewa, harin da Amurka ta kai a kan sansanin sojinta a yau yazo domin taimakon ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, da jijjifin safiyar jiragen yakin Amurka sun yi lugudan wuta a kan wani sansanin sojin kasar Syria tare da kasha mutane a wurin da kuma lalata wasu kayan yaki.

A nata bangaren rundunar sojin Syria ta bayyana hare-haren na Amurka a matsayin wani yunkuri na neman kai daukin gaggawa ga 'yan ta'addan ISIS da Nusra Front, wadanda suke shan kashi a hannun dakarun Syria.

A kan hakan Amurka ta shiga da kanta domin taimaka ma ‘yan ta’adda ta hanyar fakewa da shirin da suka shirya kuma suka aiwatar da shi,na kashe mutane da sanadarai masu guba, tare da dora alhakin hakan a kan gwamnatin Syria kamar yadda suka saba yi.

Sun yi hakan ne kuma domin samun hujja wajen shiga cikin Syria bayan da 'yan ta'addadan takfiriyyah da suka turo zuwa Syria domin kifar da gwamnatin kasar suka kasa yin hakan tsawon shekaru shida ajere.

Bayanin ya ce munanan hare-haren da ISIS suka kaddamar a yau a cikin Homs jim kadan bayan harin Amurka, ya tabbatar da hadin gwiwar da ke tsakaninsu.

A daidai lokacin da kasashe masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Syria suke nuna murna da goyon bayansu a kan wanan hari, kasashe masu yancin siyasa sun yi Allawadai da hakan.

3587494


captcha