IQNA

Mufti Na Saudiyya: Azhar Da Malamanta Maha’inta Ne

22:39 - May 03, 2017
Lambar Labari: 3481461
Bangaren kasa da kasa, babban malamin masarautar ‘ya’yan saud ya kira cibiyar muslunci ta Azhar da malaman da ke cikinta da cewa maha’inta ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin tashar alalam ya bayar da rahoton cewa, Abdulaziz bin Abadullah Al Sheikh babban mai bayar da fatawa na masarautar ‘ya’yan Saud, ya bayyana cibiyar Azhar da malanta da cewa ba suna wakiltar addinin muslunci ba ne.

Ya bayyana hakan ne sakamakon ganawar da ta gudana a tsakanin babban malamin Azhar da kuma paparoma Francis jagoran kiristoci mabiya darikar katolika da cewa, wannan ya sabawa addini, inda ya kira jagoran kiristocin da cewa bayahude ne.

Haka nan kuma ya bayyana cewa a tsawon tarihi Masar da wannan cibiya ta Azhar sun sha yin abubuwan da suka sabawa koyarwar muslunci.

3595985


captcha