IQNA

Mahukuntan Sudan Za Su Karfafa Ayyukan Kur'ani A Kasar

21:04 - May 06, 2017
Lambar Labari: 3481488
Bangaren kasa da kasa, Hasibu Muhammad Abdulrahman mataimakin shugaban Sudan ya bayyana cewa za su karfafa ayyukan kula da makarantun allo.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin mujallar Nilain cewa, Hasibu Muhamad Abdulrahman mataimakin shugaban kasar Sudan, ya gana Daf'ullah Bukhait mataimakin shugaban cibiyar kula da harkokin ta kasar Sudan.

A wannan ganawa, mataimakin shugaban kasar ta Sudan ya bayyana cewa, za su dauki matakai na musamman domin karfafa makarantun allo a kasar, kasantuwar cewa suna da muhimamnci matuka wajen yada koyar da karatun kur'ani a cikin al'umma.

Ya kara da cewa, bisa la'akari da cewa tsarin makarantun alla a kasar ta Sudan ya sha banban da tsarin makarantun zamani da suke koyar da kur'ani ta hanyoyi na zamani, wannan ya sanya ala tilas a taimaka ma makarantun na allo da wasu hanyoyi da za su taimaka musu daidai da irin tsarinsu.

Makarantun kur'ani na allo a kasar Sudan har yanzu suna bin tsohon tsari wajen koyar da karatun kur'ani, inda akan yi rubutu a kan allo, bayan karanta shin a tsawon lokaci sai a wanke domin rubuta a yoyi nag aba.

Wannan tsari na da tarihi a bangaren karatun kur'ani a kasar ta Sudan da ma wasu daga cikin kasashen Afirka, musammam kasashen yammacin nahiyar.

3596262

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha