IQNA

Bude Gasar Kur’ani Ta Malaysia / Tsawon Kwanaki 5

23:11 - May 15, 2017
Lambar Labari: 3481516
Bangaren kasa da kasa, a yau ne aka bude taron gasar kur’ani mai tsarki ta duniya karo na hamsin da tara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta daga birnin Kualalampoir cewa, a yau ne aka gudanar da bukin bude gasar ta 59 da kimanin kaarfe 20:00 agogon kasar, wato karfe 16:30 agogon Tehran, a babban dakin taron PWTC, tare da halartar minister mai kula da harkokin addini na kasar.

Wadanda suka fara gudanar da gasar su ne, Taha Izzat Bisyuni Iwad Ibrahim daga Masar, Khairu Nisa Hasani Ajas, daga Indonesia, Muhsana bint Yusuf daga Myanmar, Ilyals Kiliar daga Spain, sai kuma Muhamidin Aumfogh daga Phalipines, Yusuf Abduv daga Rasha.

Hamid Alizadeh daga Iran ya gabatar da karatun kur’ani mai tsarki a yau a r4anar farko ta bude wannan babbar gasa ta kasa da kasa a kasar Malaysia, wadda za ta kawo karshe a ranar Juma’a mai zuwa.

Makaranta kur’ani 24 ne daga kasashe 24 za su kara da juna da kuma makaranta mata guda 10 a gasar ta Malaysia, kamar yadda a bangaren harda maza 20 ne da kuma mata 10.

3599848


captcha