IQNA

Ana Zargin Malamin Kirista Da Kone Injila A Uganda

19:38 - June 01, 2017
Lambar Labari: 3481572
Bangaren kasa da kasa, Aluwesyos Bugingo daya daga cikin manyan malaman kirista a kasar Uganda an azarginsa da kone littafin Injila.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, babbar majalisar malaman addinin kirista ta kasar Uganda ta sanya wannan malamin kirista wanda mamba ne na majalisar a karkashin tuhuma, bisa zarginsa da kone littafin da suke girmamawa.

Wasu daga cikin wadanda suke aikia karakshinsa ne suka fara bayar da labarin ga sauran mutane, wanda hakan ya harzuka manyan malamain addinin kirista a kasar ta Uganda.

Yanzu haka dai an kiraye domin jin ta bakinsa kana bin da ya faru, amma ya musunta hakan, sai dai shedun gani da ido sun bayar sheda kana bin da suka ganewa idanunsu, kamar yadda kuma wasu suka dauki hoton bidiyo a lokacin da yake yin hakan.

Simon Peter Mukama shi ne ministan harkokin wajen a kaar ta Uganda, ya sheda wa daya daga cikin manyan jaridun kasar cewa, an mika wannan batu ga kotu domin ta yi bincike kuma ta bi kadun lamarin.

Ya kara da cewa, faifan bidiyo na wannan malamin kirista da ak ayi ta yadawa ta hanyoyin yanar gizo da kuma shafukan zumunta, shi ne babban abin da ya kara harzuka jama'a kana bin da ake zarginsa da aikatawa.

3605387

captcha