Baya ga taswirar masallatai da suke cikin kasashen duniya, haka nan kuma an nuna taswirar ta wasu daga cikin muhimman makarantu da kuma cibiyoyin ilimi da kuma na bincike a kan addinin muslunci a da suke a cikin wadannan kasashe.
Wadnnan alluna dai da suke dauke da taken (ni musulmi ne) suna nuna adda musulunci ya yadu a cikin dukaknin sassa na duniya, ta yadda babu wata nahiya a halin yanzu da babu musulmi a cikinta, da hakan ya hada da nahiyar Asia, da kuma nahiyar turai, Afirka da kuma Amurka.