IQNA

Ciyar Da Musulmi Masu Azumi A Jahar Kaduna

23:23 - June 06, 2017
Lambar Labari: 3481586
Bangaren kasa da kasa, wata majami’ar mabiya addinin kirista ajahar kaduna da ke tarayyar Najeriya tana bayar da abincin buda baki ga mabiya addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar The Nation da ake bugawa a tarayyar Najeriya cewa, yahanna Buru malamin addinin kirista a jahar Kaduna, shi ne ya dauki nauyin wannan shiri.

A zanatawarsa da manema labarai, Buru ya bayyana cewa, majami’arsu har kulum tana kokarin ganin an samar da yanayi na taimakekeniya a tsakanin mabiya addinai a Najeriya musamman musulmi da kirista.

A kan haka ya ce lokacin azumi lokaci mai matukar muhimmanci wanda musulmi suke dukufa wajen ibadar ubangiji, saboda haka wajibi a kan ‘yan uwansu kiristoci su nuna musu goyon baya da kuma taimaka ma musulmi marassa karfi a lokaci wannan ibada mai muhimmanci.

Ya ce wannan yasa suka dukufa wajen ganin sun tana taimako domin bayarwa ga msuulmi a wannan lokaci, musamman kayayykin da za su taimaka wajen buda baki.

Haka nan kuma ya yi kira ga masu kudi daga cikin muuslmi da kiristoci da su yi amfani da wannan damar wajen taimaka ma marassa karfi da marayu a cikin wannan wata musamman, kuma wannan ya zama aiki ne domin Allah wanda za a ci gaba da yinsa a kasa baki a sauran lokuta wadanda ban a watan Ramadan ba.

3606726


captcha