IQNA

Taron Nuna Goyon Baya Ga Al’ummar palastine A Ghana

23:37 - June 06, 2017
Lambar Labari: 3481587
Bangaren kasa da kasa, kungiyar masu ra’ayin socialists za su gudanar da wani taron nuna goyon baya ga al’ummar Palastine a kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, masu rayin socialists a kasar Ghana za su shirya gudanar da wani zaman taro a kasar domin nuna goyon bayan ga al’ummar Palastinu da ke fama da danniya da zalunci daga haramtacciyar kasar Isra’ila.

Bayanin ya ce, wannan taro zai samu halartar masana daga kasashen nahiyar Afirka daban-daban, inda za a gabatar da laccoci da kuma rubutattun kasidu, wadanda za su bayyana irin halin da al’ummar Palastine ke ciki.

Haka nan kuma sanarwar ta ce yanzu haka wasu daga cikin masana daga wasu kasashen Afirka sun riga sun sanar da shirinsu na halartar wannan taro, kamar yadda kuma aka aike da goron gayyata ga ‘yan siyasa da kungiyoyi masu zaman kansu a kasashen Afirka daban-daban.

Babbar manufar wannan taro dai ita ce it ace tausaya ma mutanen da ake zalunta da kuma sanar da duniya halin da suke ciki wanda kafofin yada labarai ba su fada wa duniya.

3606833


captcha