A jiya sun gudanar da karatu a cibiyar Rasuli Center da ke yankin Raslo a cikin birnin na Pretoria, tare da halartar mutane da dama da suka saurari karatun nasu da kuma tawashi na bege manzo.
Waann tawaga dai ta isa kasar Afirka ta kudu ne da nufin kara karfafa musulmi a kan harkokin addini da kur'ani mai tsarki, karkashin kulawa cibiyar kula da harkokin al'adun musulunci ta jamhuriyar musulunci ta Iran.