IQNA

Ghasemi Ya Yaddada Cewa:

Iran A Shirye Ta Taimaka Ma Makwabta Domin Murkushe 'Yan Ta'adda

17:42 - July 01, 2017
Lambar Labari: 3481659
Bangaren kasa da kasa, kakakin ma'aikatar harkokin kasar Iran Bahram Qasemi ya mika sakon taya murna ga jagororin kasar Iraki da al'ummar kasar baki daya kan nasarar murkushe 'yan ta'adda.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Bahram Qhasemi ya bayyana nasarar da dakarun Iraki suka samu a kan 'yan ta'adda da cwa babbar nasara ce ta tarihi.

Ya ce ko shakka babu dakarun Iraki tare da dukkanin goyon bayan da al'ummar kasar suka bayar wajen ganin kawo karshen daesh a kasar babbar nasara ce ga dukkanin al'ummar yankin gabas ta tsakiya, domin an karya babban lago na wadannan 'yan ta'adda da suka addabi yankin.

Ya kara da cewa a kowan elokaci Irana shirye take ta ci gaba da taimaka ma Iraki da ma sauran kasashen yankin gabas ta tsakiya wajen yaki da 'yan ta'adda, domin al'ummar wannan yanki ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Daga karshe ya yi kura a kan cewa, wajibi ne akan dukkanin kasashen yankin su dauki matakai na dakushe dukaknin hanyoyin da 'yan ta'addan suke samun goyon baya baya na kudade da makamai da kuma wanke kwakwalensu da ake yi ana dora su kan wanann mummunar akida, idan ba a kawo karshen wadannan abubuwa to har yanzu da sauran aiki.

3614010


captcha