IQNA

Faifan Bidiyo Mai Taken Gwagwarmaya Da Kuma Kyamar Sahyuniya Ya Samu Karbuwa

23:56 - July 10, 2017
Lambar Labari: 3481688
Bangaren kasa da kasa, wani faifan bidiyo da aka fitar a shafukan yanar gizo mai taken gwagwarmaya da kuma kyamar sahyuniyawa ya samu gagarumar karbuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga ofishin yada al’adun muslunci na Iran a Lebanon cewa, Hadi Za’arur ne ya hada wannan faifan bidiyo kuma ya saka shi a cikin shafukan yanar gizo.

Bayan saka wannan faifan bidiyo wasu daga cikin ‘yan gwagwarmaya daga Gaza sun aike da sakonninsu na nuna farin ciki da wanann kira na ci gaba da gwagwarmayar neman ‘yanci da kuma kin amincewa da zaluncin Sahyuniyawa.

Daga saka faifan bidiyon kasa da mako guda, ya samu mutane fiye da miliyan daya da suka duba shi tare da saka alamar sun ji dadin hakan.

Babbar manufar samar da wannan bidiyo dai ita ce kara fadakar da al’ummomin duniya dangane da halin da al’ummar Palastinu ke ciki na danniya da zalunci da suke fuskanta daga yahudawan sahyuniya, da kuma wajabcin taimaka musu.

Da dama daga cikin jaridun yahudawan Isra’ila sun mayar da martani a kan wannan faifan bidiyo, tare da bayyana shia matsayin wani sabon yunkuri na kawar da Isra’ila ta wata sabuwar hanaya.

Za aiya kallon video nan:-

3617357


captcha