Bayanin ya ci gaba da cewa kungiyar ta hada wasu daga cikin yahudawa masu tsatsauran ra'ayin akidar yahudancin sahyuniya, da suke tsananin kiyayya da musulmi, wanda kuma suke samun cikakken goyon baya daga gwamnatin Isra'ila.
A cikin 'yan kwanakin nan dai a kullum rana wani gungu daga cikin mabiya kungiyar sun kutsa kai a cikin masallacin quds domin tsokanar musulmi, da kuma keta alfarmar wannan wuri mai tsarki, a lokaci guda kuma 'yan sanda yahudawan sahyuniya na ba su kariya.
Yanzu haka dai daruruwan matasan Palastinawa ne suka yi cincirindo a kusa da masallacin quds domin hana yahudawa kutsa kai a cikinsa, duk kuwa da cewa jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila na yin amfani da karfi domin tarwatsa su.