IQNA

An Yanke Hukunci A Kan wani Mai Barazana Ga Musulmi A Landan

21:16 - August 05, 2017
Lambar Labari: 3481770
Bangaren kasa da kasa wato kotu a birnin Landan na kasar Birtaniya a cikin unguwar Cricklewood a yankin Brent a Landan ta yanke hukunci kan mai yin barazanar kisa a kan musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin jaridar Times ya bayar da rahoton cewa, david Mofatt dan shekaru 39 da haihuwa, ya fukanci hukunci a kotu, na gudanar da aiki sa'oi 100 ba tare da albashi ba, da kuma biyan tara har fan 705.

Wannan hukunci dai ya zo sakamakon barazanar da ya yi a kwanakin baya a yankin Cricklewood, inda ya yi ta kururuwa yana mai yin kira da a kashe musulmi, yana mai cewa zai tarwatsa shagon sayar da littafai na musulmi da ke wurin.

Madlin Rider ita ce babbar jami'ar 'yan sanda a bangaren gudanar da bincike ayankin, ta bayyana cewa ba su taba amincewa da ayyukan nuna kyama ga musulmi ba, a kan duk wanda ya aikata irin wannan zasu shiga kafar wando daya da shi.

3626710


captcha