Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoto n cewa, bangaren
hulda da jama'a na cibiyar yada al'adun muslunci ta kasar ya sanar da cewa, Fallah
Pisheh shugaban ofishin yada al'adun muslunci a Afirka ta kudu ya ce, a yau ne
za a watsa wani shiri dangane da ayyukan kur'ani da Iran take gudanarwa a
Afirka ta kudu a tashar Rasad ta kur'ani kai tsayi.
A Larabar da ta gabata ma an saka wani shiri makamncin haka tare da shugabannin ofisoshin yada al'adun muslunci na Iran a kasashen Girka Ali Muhammad Helmi, Ali Asgar Amiri na Bosnia, Ali Bakhtiyari Uganda, Abdul Ridha Saifi, da kuma mataimakin shugaban ofishin akasar Indonesia.
Dukkaninsu sun gabatar da bayanai da kuma nuna irin ayyukan da ake gabatarwa ta fuskacin ayyukan kur'ania kasashen da suke wakiltar jamhuriyar musulunci ta Iran.