IQNA

Musulmin Barcelona Na Cikin Damuwa

21:56 - August 20, 2017
Lambar Labari: 3481816
Bangaren kasa da kasa, musulmi mzauna birnin Barcelona na kasar Spain suna cikin damuwa tun bayan harin ta’addancin da aka kai a birnin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa, tun bayan harin ranar Alhamis da ta gabata da aka kai a cikin birnin Barcelona, musulmi a nirnin suke cikin tsoro.

Raja Miyah shi ne limamin wani masallaci da ke tsakiyar birnin na Barcelona ya bayyana cewa, tun bayan kai harin adadin musulmi masu zuwa salla a masallacin ya ragu matuka, domin kuwa suna jin tsoron cewa a kowane lokaci za a iya kawo ma masallacin hari da sunan daukar fansa a kan musulmi.

Ya kara da cewa, suna gudanar da sallar idi a kowace shekara a masallacin, amma a wannan karon ga dukkanin alamu musulmin da za su zo sallar idin babbar salla kadan ne, saboda halin da ake ciki a yanzu tun bayan kai harin.

A ranar Juma’a da ta gabata, wasu gungun musulmi a birnin na Barcelona sun gudanar da wani gangami, inda suka yi tir da Allah wadai da harin da ‘yan ta’adda suka kai a birnin, tare da nisanta kansu dama addinin msulunci daga wannan mummunan aiki.

Kungiyar ‘yan ta’addan Daesh dai ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin kaddamar da harin, wanda yay i sanadiyyar mutuwar mutane 13 dukkaninsu fararen hula, tare da jikkatar wasu da dama.

3632246


captcha