IQNA

Kungiyar Kasashen Kasashen Musulmi Ta Yi Kakkausar Kan Kisan Musulmi A Myanmar

23:51 - August 30, 2017
Lambar Labari: 3481847
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta fitar da wani bayani da ke yin tir da Allah wadai da kakkausar murya dangane da kisan kiyashin da ake yi wa msuulmi a kasar Myanmar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kngiyar kasashen musulmin ta fitar, ta bayyana kisan gilla da kuma gallazawar da ake yi wa msuulmin kasar Myanmar da cewa ba abu ne da za a aminta da shi ba.

Bayanin ya ci gaba da cewa, dukkanin dalilai sun tabbatar da cewa jami’an soji da kuma ‘yan sandan gwamnatin Myanmar sunha da hannu kai tsaye a kisan kiyashin da ake yi wa musulmin wannan kasa, tare da rusa musu gidaje da kone musu kaddarori da kuma fitar da su daga yankunansu da karfin tuwo, baya ga kisan mata da kanan yara da kone gawwawkinsu.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, a cikin ‘yan kwanakin nan an kasha muslmi fiye da 100 tare da tilasta wasu fiye da dubu 20 barin muhallansu, inda sojojin gwamnatin kasar ta Myanmar da ‘yan sanda suke aikata hakan gami da masu tsatsauran ra’ayin addinin Buda.

Daga karshe kungiyar kasashen musulmin ta kirayi gwamnatin Myanamr da ta gaggauta kawo karshen wannan kisan kisan kiyashi a kan musulmi ba tare da wani bata lokaci ba.

3636241


captcha