Kamfanin dilalncin labaran iqn aya bayar da rahoton cewa, mahajjata sun fara aikin hajjin a jiya, kuma jami'an tsaro suna taimakawa yan sanda hanya don tabbatar da cewa babu wata matsala sanadiyyar cinkoson mutane
A safiyar yau Alhamis ne mahajjatan zasu tsaya a filin mina kusa da dutsen Jabal Rahama inda zasu yi yi suna addu'o'i da kuma tawaliu ga ubangiji har zuwa magarima a lokacinda zasu kwarara zuwa mash'aril Haram inda zasu bada sallolin magariba da issha. Sai kuma gobe salla mahajjatan zasu fara jifan shaidan.
A bangaren kiwon lafiya kuma hukumomin sun ajiye ma'aikatan bada agajin gaggawa na Hilal Ahmar a ko wani lungu da sako da mani da kuma arafa don bada taimakon gaggawa a duk lokacinda wata matsala ta taso.