IQNA

Mutane Uku Ne Suka Rasa Rayukansu A wurin Sallar Idi A Najeriya

23:31 - September 02, 2017
Lambar Labari: 3481857
Bangaren kasa da kasa, sakamakon wani hadarin mota da ya wakana a cikin jahar Ogun a Najeriya, mutane uku ne suka rasa rayukansu a wurin sallar idi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na vanguardngr cewa, Abimola Owemi jami’i mai kula da huldar jama’a na rundunar ‘yan sanda a jahar Ogun ya bayyana cewa, wani direban mota ne ya haddasa hadarin

Bayan faruwar lamarin mutane uku sun rasa rayukansua na take a lokacin gudanar da sallar, lamarin ya fusata jama’a har suka nemi daukar fansa a kansa, amma jami’an ‘yan sanda suka shiga tsakani.

A ranar Juma’a ce3 dai a ka gudanar da sallar idi a Najeriya inda akasarin mutanen kasar miliyan dari da kusan casa’in musulmi ne, wasdanda suka fi yawa a arewa.

An bayar da hutun salla a ranar Juma’a yain da kuma ranakun Asabar da Lahadi hutu ne a fadin kasar baki daya.

3637201


captcha