IQNA

21:33 - September 07, 2017
Lambar Labari: 3481873
Bangaren kasa da kasa, an bukaci mahukuntan jahar Abiya a tarayyar Najeriya da su gina makabartar musulmi a cikin jahar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar vanguard da ke bugawa a Najeriya ta bayar da rahoton cewa, Musa Aihakarim shugaban kungiyar muuslmi mazauna jahar Abiya ya gabatar da bukatar neman a gina wata makabarta ta musulmi a cikin jahar.

Ya bayyana cewa sun bukaci hakan ne daga gwamnan wannan jaha, sakamakon matsaloin da musulmi suke fuskanta a jahar na rashin makabarta wadda za a rufe gawawwakinsu idan Allah ya yi musu rasua.

Ya kara da cewa yanzu haka akwa gawawwakin wasu musulmi da suka rasa raykansu su shida da ba a rufe su, sakamakon babu inda za a rufe su, domin dukkanin makabartun na kiristoci ne, kuma ba a su bari a bizne musulmi a ciki ba.

Tarayyar Najeriya dai na daga cikin kasashen nahiyar Afirka da suke da musulmi da kiristoci a jahohin kasar, amma muuslmi sun fi yawa a arewaci, yayin da kua a kudanci mabiya addinin kirista suka fi yawa.

3639606


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: