Ya ce ko shakka babu addinin buda bai yarda da kisan jama'a ma ba gaira ba sabar, domin kuwa musulmi 'yan kasar Myanmar 'yan kabilar Rohingya babu wani laifi da suka yi wa wani balantana a kasha su haka kisa na wulaknci da tozarci.
Haka nan kuma ya kirayi firayi minister kaar ta Myanmar Suu Kyi da gaggauta daukar matakin ganin an dakatar da wannan mummunan aiki da ak eyia kasar da sunan addinin buda, kuma su samo hanyoyin yin sulhu da zaman lafiya atsakanin dukkanin al'ummar kasar.
Dalai Lama ya ce hakika hankalinsa ya tashi matuka dangane da kisan da ake yi musulmi Myanmar, da kuma yadda ake tozarta su da ci musu zarafi, inda yace hakaki na yana cikin bakin maras misiltuwa akan wannan mummunan aiki.
Tun daga lokacin da 'yan addinin buda tare da sojojin gwamnatin Myamanr suka fara yin kisan kiyashi a kan musulmi a kasar kimanin makonni uku da suka gabata, yazu yanzu an kasha dubai tare da raunata wasu, wasu kuma sun tsere sun bar gidajensu.