Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, shafin yada labarai na Kafil ya habarta cewa, an gudanar da taron ne tare da halartar dubban mutae daga sassa na kasar da suka halarci wannan wuri mai tsarki a karbala.
A yayin dora wannan tuta, jami’an gwamnati da kuma ma’akkatan wurin gai da wasu daga cikin malamai sun halarci wuri.
Bisa ga alada akan dora wannan tuta ne ‘yan kwanaki kafin lokacin gudanar da tarukan Ashura, inda miliyoyin mutane daga ciki da wajen kasar ta Iraki suke halarta.
An dra tutocin biyu ne a kan hubbarorin mam Husan (AS) da kuma Abu fadl Abbas (AS) alamar da ke nuna da karatowar lokacin gudanar da tarukan ashura, daya daga cikin babbar rana da mabiya tafarin iyalan gidan manzon Allah ke yin juyayin kisan Imam Hussain da zuriyar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa.