Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da
rahoton cewa, a jiya an Sheikh Jalal shi ne shuagaban makarantar Imam Sadiq (AS) kuma shi ne ya gabatar da jawabia wurin tare da halartar mabiya tafarkin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
An gabatar da jawaban ne a cikin harsunan farisanci da larabci kasantuwar cibiyar tana gudanar da wani shiri na koyar da harshen farisanci a wurin ga dalibai da dama, wadanda a halin yanzu suna fahimtar harshen.
Shugaban karamin ofishin jakandancin Iran tare da wasu daga cikin malamai sun halrci wurin gudanar da wannan taron makoki.