Shafin Ashura.info shi ne bababn shafi na wannan shiri wanda iya shiga kuma ya isar da sakon Imam Hussain ta hanyar da zai iya ga al'ummar musulmi na duniya.
Masu aitawatar da wannan shiri suna yin amfani da farar takarda da ake rubuta sayYahussein# wato kace ya Hussain da nufin yada sunan wannan mutum mai daraja a tsakanin al'ummomin domin sanin darussan da suke tattare da sadaukarwar da ya yi domin kare 'yanci da kuma dukkanin al'ummomin da ake zalunta a tsawon tarihi.
Ko shakka babu wannan shiri ya samu karbuwa matuka musamman idan aka yi la'akari da yanayin al'ummar Amurka wadda bata da alaka da addini sosai hatta wadanda suke kiristoci wadanda su ne suka fi yawa akasar amma bas u damu da addini ba, inda bayyana musu Imam Hussain (AS) da abin da ya faru da shi yana yi musu tasiri.