Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Kafil ta bayar da rahoton cewa, birnin karbala mai alfarma na cewa na fuskantar cunkoso mai tsanani a dukkanin hanyoyin da suke isa zuwa cikin garin a daidai lokacin gabatowar ranar shahadar Abul fadl Abbas.
Wannan cunkoso yana karuwa ne zuwa yau daren tasu’a, inda ake gabatar da taruka a hubbarorin Imam Hussain (AS) da kuma Abul Fadl Abbas (AS).
Bisa ga al’ada dai miliyoyin mabiya tafarkin ahlul bait ne har ma da sauran musulmi mabiya wasu mazhabobin daban sukan halarci wannan wuri mai albarka alokacin gudanar da tarukan ashura, kasantuwar Imam Hussain ya yi sadaukantarwa ne domin wanzuwar addinin muslunci, da kuma wanzuwar ‘yanci ga dukkanin bil adama.
Jami’an tsaro gami da masu taimaka musu sun kafa shingaye a dukkanin hanyoyin da ke isa birnin, kamar yadda haka lamarin yake a cikin dukkanin yankunan birnin.