IQNA

Iraniyawa Miliyan 3 Ne Za Su Halarci Ziyarar Arbaeen

21:11 - October 29, 2017
Lambar Labari: 3482048
Bangaren kasa da kasa, Mir Masud Husainiyan shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a Karbala da ke kasar Iraki ya bayyana cewa Iraniyawa miliyan uku ne za su halarci ziyarar arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo naSaymaria News cewa, Mir Masud Husainiyan shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a Karbala da ke kasar Iraki ya bayyana a gaban taron manema labarai a jiya cewa, masu ziyara daga Iran mliyan 3 za su halarci ziyarar arbaeen a birnin karbala mai alfarma.

Ya ci gaba da cewa ya zuwa an tanadi kayan aiki a bangaren kiwon lafiya, inda daruruwan kwararrun likitoci za su kasance a cikin tawagar domin kula da jama’a, inda za a saar da rukuni guda 10 na likitoci da kayan aiki.

Dangane da karbar izinin shiga cikin kasar Iraki kuwa, ya bayyana cewa ya zuwa jiya an bayan da biza ga mutane miliyan daya da dubu 270, kuma ana ci gaba da bayarwa, wanda adadin wadanda za su samu biza zai kai miliyan uku.

3657919


captcha