IQNA

An Cafke Wasu ‘Yan Ta’adda Na Shii Kai Kan Masu Ziyarar Arbaeen

23:07 - November 09, 2017
Lambar Labari: 3482083
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Iraki sun samu nasarar cafke wasu ‘yan ta’adda a lokacin da suke shirin kai kan wasu masu tafiya ziyarar arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saumaria cewa, jami’an tsaron kasar Iraki masu gudanar da ayyukan a lokacin tarukan arbaeen, sun samu nasarar cafke wasu ‘yan ta’addan wahabiya a lokacin da suke shirin kai kan wasu masu tafiya ziyarar arbaeen a yankin Suwara.

Mutanen dai suna tafiya ne akasa a kan hanyarsu ta zuwa birnin karbala omin halatar tarukan arbaeen na Imam Hussain (AS) inda ‘yan ta’addan suka kutsa cikinsu suka batar da sawu, amma da ikon Allah an gano su.

Jami’an tsaron Iraki sun samu nasarar cafke su tare hana su hasu tayar da bam da suka shirya domin kasha adadi mai yawa na masu gudanar da ziyarar.

‘Yan ta’addan wahabiya suna hankoron ganin sun kawo cikas ga duk lamari da ya shafi ahlul bait da ake gudanarwa a cikin kasar Iraki, musamamn ma wanda ya shafi Imam Hussain amincin Allah ya tabbata a gare shi.

3661646


captcha