IQNA

An Dakatar da Gudanar Da Tarukan Maulidi Kan Tituna A Alkahira Masar

21:34 - November 29, 2017
Lambar Labari: 3482150
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar mabiya darikun sufaye a kasar Masar ta sanar da dage tarukan maulidin amnzon Allah da ta saba gudanar a kan titunan birnin Alhakira.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Egyptian Street cewa, babbar cibiyar mabiya darikun sufaye a kasar Masar ta sanar da dage tarukan maulidin amnzon Allah da ta saba gudanar a kan titunan birnin Alhakira a kowace shekara.

Ahmad Kandil kakakin gamayyar kungiyoyin sufaye da dariku a Masar yace, bisa ga al'ada dai mabiya darikun sufaye da ma sauran musulmi masoya manzon Allah (SAW) suna gudanar da bukukuwan maulidin amnzon Allah a kan manyan titunan birnin Alkahira tsawon daruruwan shekaru.

Kungiyar ta sanar da haka ne sakamakon harin ta'addancin da wahabiyawan takfiriyya suka kaddamar kan masallacin Raudha a ranar Juma'a da ta gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 305.

Bayan kai wannan harin ta'addanci, shugaban kasar Masar Abdulfattah Sisi ya sha alwashin shiga kafar wando daya da 'yan ta'addan wahabiyawa.

3667961


captcha