IQNA

20:41 - December 02, 2017
Lambar Labari: 3482158
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da sallar juma’a ta farko a masallacin Raudha a kasar Masar bayan harin ta’adancin da wahabiyawa suka kai kan musulmi a lokacin sallar Juma’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a jiya an gudanar da sallar Juma’a ta farko a masallacin Raudha da ke garin Alarish a yankin Sinai na a kasar Masar bayan harin ta’adancin da wahabiyawa suka kai kan musulmi a lokacin sallar Juma’a a makon da ya gabata.

Bayanin ya ce bayan harin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar masalata fiye da 300 da jikatar wasu daruruwan, a jiya an ci gaba da gudanar da salla a wannan masallaci na ‘yan darika, wanda wahabiyawa suka kai wa harin ta’addanci.

Jami’an tsaro a ckin kayan sarki ne suke bayar da kariya tare da tabbatar da tsaro a kan dukkanin hanyoyin da k isa masallacin, kamar yadda kuma hatta a cikin masallacin jami’an tsaro suna sanya ido domin kare rayukan masallata.

Tun bayan kifar da gwamnatin Muhammad Morsi, wahabiyawa suke tayar da fitina a yankin Sinai a na kasar Masar, inda suke kaddamar da hare-haren ta’addanci da bama-bamai, tare da kai hari a kan masallatai na musulmi da suke kafurtawa.

3668671


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: