IQNA

Jagora Yayin Ganawa Da bakin Taron Makon Hadin Kai:
23:37 - December 06, 2017
Lambar Labari: 3482172
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar kokarin da Amurka ta ke yi na mayar da birnin Qudus a matsayin helkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila wata gazawa ce daga bangarensu don kuwa matsalar Palastinu wani lamari ne da ya fi karfinsu.

Fir’aunan Amurka Da Sahyuniyawa Hankoronsu Shi Ne Tarwatsa Gabas Ta TsakiyaKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar kokarin da Amurka ta ke yi na mayar da birnin Qudus a matsayin helkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila wata gazawa ce daga bangarensu don kuwa matsalar Palastinu wani lamari ne da ya fi karfinsu, yana mai jaddada cewar ko shakka babu za a 'yanto kasar Palastinu daga mamayar sahyoniyawa.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a yau din nan Laraba a wata ganawa da yayi da manyan jami'an kasar Iran da kuma baki mahalarta taron Makon Hadin Kai na kasa da kasa da aka gudanar a nan Tehran don tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah (s) da jikansa Imam Sadiq (a.s) inda ya ce makiyan dai babu wani abin da za su iya don kuwa lamarin Palastinu ya riga da ya fice daga hannunsu.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa siyasar Amurka a yankin Gabas ta tsakiya ita ce haifar da fitina da yake-yake don tabbatar da tsaro da zaman lafiyar haramtacciyar kasar Isra'ila, to sai dai abin bakin cikin shi ne a halin yanzu ana samun wasu shugabanni da 'yan siyasa da suke taimakon Amurka wajen cimma wannan manufa nata.

Jagora Imam Khamenei dai yana mayar da martani da kalaman shugaban Amurka Donald Trump wanda a jiya ya sanar da shugaban Palastinawa Mahmood Abbas aniyarsa ta mayar da ofishin jakadancin Amurka da haramtacciyar kasar Israilan zuwa birnin Qudus daga Tel Aviv lamarin da ke ci gaba da fuskantar tofin Allah madaukakin sarki.

3669934

 

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: