IQNA

16:15 - December 14, 2017
Lambar Labari: 3482200
Bangaren kasa da kasa, majalisar birnin Dublin fadar mulkin Ireland ta kada kuri'ar kwace lambar yabo da ta baiwa shugabar kasar Myanmar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Guardian ta kasar Birtaniya cewa, a jiya majalisar birnin Dublin fadar mulkin Ireland ta kada kuri'ar kwace lambar yabo da ta baiwa shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi.

Wannan kada kuri'a ya zo ne sakamakon irin kisan kiyashin da ake yi 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar a karkashin gwamnatin Aung San Suu Kyi, wadda sojojin gwamnatinta ne suke aiwatar da wanann mummunan aiki tare da 'yan addinin buda  akan musulmi.

'Yan majalisar 59 suka amince da hakan yayin da 2 ne kawai suka ki amincewa, inda za a amshe lambar yabo ta dimuradiyya da majalisar ta bata a shekarun baya.

Bayanin 'yan majalisar ya ce an dauki wannan matakin ne domin nuna rashin amincewa da abin da ake yi musulmi 'yan kabilar Rohingya  a kasar Myanmar a karakshin gwamnatin Aung San Suu Kyi, wadda take raya kare hakkin bil adama da adawa da zalunci.

Inda yanzu haka fiye da mutane dubu 620 ne suka yi gudun hijira zuwa wajen kasar domin tsira da rayukansu, sakamakon kisan gillar da ake yi wa 'yan uwansu.

3672648

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: