IQNA

22:35 - December 23, 2017
Lambar Labari: 3482228
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsai ta kasar Amurka a birnin Chicago.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yada labarai na masicna cewa, ana shirin gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsai ta kasar Amurka a birnin Chicago da nufin karfafa hardar kur’ani a tsakanin matasan msuulmi na irnin.

Wannan gasar hardar kur’ani za ta hada matasa masu shekaru daban-daban, kamar yadda gasar za ta kunshi bangaren juzui na 25, da juzui na 20, sai juzui na 15, da juzi na 10 da kuma na 5, sai juzui 1 wanda ya shi ne bangaren karshe.

A cikin wwannan mako ne musulmin Amurka za su gudanar da babban taronsu na shekara-shekara, wanda cibiyar MAS za ta shirya, wanda zai samu halaratr dubban mauusulmi dacwakilan kungiyoyi da cibiyoyinsu daga dukkanin yankuna na arewacin Amurka.

Baya ga wannan gasar gasar kur’an da za a gudanar, akwai jawabai da malamai da kuma masana za su gabatar a kan tarihin manzon Allah da kuma darussan da suke cikin rayuwarsa mai albarka.

3675239

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: