IQNA

23:37 - December 24, 2017
Lambar Labari: 3482231
Bangaren kasa da kasa, majiyoyin gwamnatin palastine sun tabbatar da cewa, tun bayan kudirin da Trump ya dauka na amincewa da quds a matsayin babban irnin yahudawa, palastinawa sha biyar sun yi shahada.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ma'aikata kiwon lafiya ta Palasdinu ta sanar da shahadar Muhammad Sami Dahduh sanadiyyar harbin da 'yan sahayoniya suka yi masa.

Cibiyar tattara bayanai ta Palasdinu ta kuma kara da cewa wani matashin bapalasdine wanda ya jikkata a harin da yan Sahayoniya suka kai masa a makon da ya wuce a gabacin Jabaliya, ya yi shahada a yau lahadi.

Yahudawa 'yan share wuri zauna da sojoji suke goyawa baya sun kai hari a kauyen Madama da ke kudancin Nablus tare da jikkata palasdinawa shida.

Makwanni biyu a jere kenan da palasdinawa suke gudanar da Zanga-zangar nuna kin amincewa da matakin shugaban kasar Amurka na bai wa 'yan Sahayoniya birnin kudus a matsayin birninsu.

3675817

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: