IQNA

16:41 - December 27, 2017
Lambar Labari: 3482241
Bangaren kasa da kasa, an kammala dukkanin shirin gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta Khartum a kasar Sudan a karo na tara.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na cibiyar ayyukan kur'ani Sudan ya bayar da rahoton cewa, Mu'az Fatih Alhaj ya bayyana cewa, ya zuwa an kammala dukkanin shirin gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta Khartum a kasar Sudan a karo na tara, tare da halartar masu gasa su 70 daga sassa na kasar.

Ya ce dukkanin wadanda za su shiga wannan gasa sun fito ne daga jahohin kasar, kuma za su kara da juna inda ga karashe za a fitar da wadada suka fi nuna kwazo domin absu kyautuka na musamman.

Haka nan kuma ya kara da cewa, za a gudanar da gasar ne a babban masallacin Annur da ke cikin birnin na Khartum, inda kuma za a rufe gasar tare da halartar manyan baki da suka hada da shugaba Umar Hassan Albashir na kasar, tare da wasu manyan jami'an gwamnati.

A shekarar da ta gabata ma an gudanar da wata gasa ta kasa da kasa karo na takwas a birnin na Khartum, tare da halar masu gasa su 74 daga kasashen 55, Muhammad Khakpour shi ne ya wakilci jamhuriyar muslunci ta Iran a wannan gasa.

3676870

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: